Fargabar barkewar yakin basasa a Masar | Siyasa | DW | 08.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Fargabar barkewar yakin basasa a Masar

Kisan kiyashin da jami'an tsaron Masar suka yi wa masu goyon bayan Mursi, ya sake tsunduma kasar cikin yamutsi.

Su dai mahukuntan na Masar, da suka nuna takaicinsu da abin da suka kira, taho-mu-gama da ta auku tsakanin wadanda ke kokarin kutsawa cikin ofishin dakarun soji a gefe daya, da kuma dakarun soji a daya gefen, lamarin da ya kai ga halakar wasu jami'an sojoji biyu da fararen hula da dama, sun yi alkawarin fara binciken musabbabin abin da magoya bayan shugaba Mursi suka kira shi kisan gillar da sojoji suka yi wa masu nuna kyama cikin lumana, da harammtacciyar gwamnatin da aka yi kwacenta ,da zimmar karya lagwansu.

"A tashin farko, sun harbe mutane 34 har lahira, kana suka ci gaba da yin barin-wuta kanmu a yayin da muke sallar Asuba. Ina gargadin janar Sissy

da ya kwan da sanin cewa, munyi rantsuwa jininmu ba zai sake tafiya a banza ba."

Shehul Azhar, shugaban addinin kasar, yayi barazanar kauracewa shiga jama'a muddin ba a yi bincike mai cin-gashin kansa da wannan aikin ta'asa ba, kana ya kara da cewa:

"Ina kira da a fara taron kasa na sasantawa a cikin kwanaki biyu masu zuwa, da kuma sakin dukkannin fursinonin siyasa, ina kira ga dukkanin 'yan kasa da su guji abin da zai kai ga zubar da jinin 'yan kasa."

Martanin jam'yyar 'yan-Uwa Musulmi ta Masar

Jam'iyyar 'yan uwa Musulmi, da tace, harin, take-take ne na razana magoya bayanta don su daina bin kadin hakkinsu da aka kwace, ta sha alwashin ci gaba da bin salon lumana har sai hakarta ta cimma ruwa, kana ta kara da yin kira ga sojojin da suke da kishi da su yi bore ga duk wani umarnin kashe farar hula da kwamandojinsu za su basu.

Kamar yadda itama jam'iyya ta biyu wajen yawan magoya baya a kasar, wato Annur ta salafiyawa, bayan da ta janye daga tattaunawar da take da fadar shugaban kasa tace, ba za ta bar jinin wadanda aka kashe ya tafi a wofi ba.

Ita kuwa gamayyar 'yan hamayyar kasar, wadanda a yanzu suke shirin kafa sabuwar gwamnati karkashin jagorancin Baha-Uddeen, kira sukai ga 'yan kasar da su guji yin taho-mu-gama da sojojin kasar, kana suka kira da a gudanar da bincike kan batun.

Wannan waki'ar da ta faru a kasar dai, a dadiadi lokacin da kasar ke cikin yamutsin siyasar dake kara dagulewa, ya sanya masharhanta na nuna fargabar tsundumar kasar cikin yakin basasa, muddin sojojin za su ci gaba da bawa wani bangaren kariya da murkushe daya bangaren.

Mawallafi : Mahmud Yaya Azare
Edita : Saleh Umar Saleh

Sauti da bidiyo akan labarin