1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'i

Pakistan: Fargabar barkewar annoba

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 31, 2022

Mahukuntan kasar Pakistamn, sun bayyana fargabarsu kan yaduwar cututtukan da ake dauka sakamakon gurbataccen ruwa a tsakanin dubban mutanen da bala'in ambaliyar ruwan da ta afku a kasar ya rutsa da su.

https://p.dw.com/p/4GHmf
Pakistan | Ambaliyar Ruwa
Fargabar yaduwar cututtuka masu nasaba da gurbataccen ruwa a PakistanHoto: DW

Likitoci a sasssa dabam-dabam na kasar da aka jibge wadanda suka tsira da rayukansu daga ambaliyar, sun nunar da cewa da farko mutanen na fama ne da matsalar firgici saboda ambaliyar. Sai dai likitocin sun bayyana cewa, a yanzu mutane da dama na fama da gudawa da cututtukan fata da sauran cututtukan da ke da nasaba da gurbataccen ruwa. Mata masu juna biyu da dama da ke yankunan da ibtila'in ambaliyar ruwan ya afku, na cikin gagarumin hadari. Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan mummunar ambaliyar ruwan da ta afku a kasar, wanda ya sanya Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci tallafin gaggawa na dalar Amirka miliyan 160 domin agazawa kasar da miliyoyin gidaje suka rushe. A cewar Hukumar Kula da Yawan Jama'a ta Majalisar Dinkin Duniya, akwai kimanin mata masu juna biyu dubu 650 da ke bukatar daukin gaggawa domin dawainiyar ciki da haihuwa cikin sauki.