Fargaban ƙasashen duniya a kan Libiya | Labarai | DW | 27.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fargaban ƙasashen duniya a kan Libiya

Manzon musammun na MDD a Libiya Martin Koblers ya bayyana rashin gajen dangana na ƙassahen duniya a kan gazawa na 'yan siyasa na Libiya na aiwatar da shirin zaman lafiya.

Martin Koblers Besuch in Libyen

Martin Koblers Manzon musammun na MDD

Hakan kuwa na zuwa ne kwanaki biyu bayan da majalisar Tobruk ta yi watsi da shirin gwamnatin haɗin kan ƙasa a Libiyar wanda aka cimma a makon jiya.Koblers wanda ke yin magana da 'yan jaridu a birnin Tunis ya ce ƙungiyar IS na ƙara danawa a yankin kudancin Sahara.


Abin da ke zaman barazana ta ƙara bazuwar aiyyukan ta'addanci a ƙasashen Chadi da Nijar sannan kuma ya ce a gobe za su gudanar da taron kan batun tare da Ƙungiyar Tarrayar Afirka a Habasha.