FARC ta rikide zuwa jam′iyya a Kwalambiya | Labarai | DW | 02.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

FARC ta rikide zuwa jam'iyya a Kwalambiya

Kimanin wakilai na kungiyar 1,200 ne suka zauna a wannan mako a birnin Bogota don tattauna batun kungiyar na sauyawa daga masu fafutika da makamai zuwa 'yan siyasa.

'Yan tawayen FARC na kasar Kwalambiya a ranar Juma'a sun bayyana kansu a matsayin jam'iyyar siyasa a hukumance, abin da ke zuwa bayan kwashe rabin karni tana gwagwarmaya da makamai. Da yake jawabi ga dubban magoya bayansa a birnin Bogota kwamandan kungiyar ta FARC Rodrigo Londono "Timochenko," ya ce nan gaba makamin yakinsu shi ne amfani da kalmomi ba bindiga ba.

Kimanin wakilai na kungiyar 1,200 ne suka zauna a wannan mako a birnin na Bogota don tattauna batun kungiyar na sauyawa daga masu fafutika da makamai zuwa 'yan siyasa da za su fita yaki da kalmomi na baka. Wannan dai na zuwa ne bayan cimma yarjejeniya ta zaman lafiya da gwamnati a shekarar bara, yarjejeniyar da ta kafa tarihi.