Farautar maharan birnin Paris | Labarai | DW | 09.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Farautar maharan birnin Paris

Maharan gidan mujallar nan ta Charlie Hebdo ta birnin Paris na Faransa sun yi garkuwa da wani mutum da ke aiki a wajen buga takardu.

Dakarun sojan yaki da ta'addanci a Faransa sun yi kawanya ga wani karamin garia arewacin kasar, yayin da jirage masu saukar ungulu ke ta shawagi a garin bayan da wata majiyar 'yan sanda ta bada rahoton cewa 'yan bindigar nan da suka kai hari a gidan mujallar nan ta Charlie Hebdo sun yi garkuwa da wani mutum da ke aiki a wajen buga takardu.

Tun da fari dai 'yan sanda sun bi wata mota aguje da ta nufi birnin Paris yayin da masu motar suka ajiyeta suka ranta cikin na kare, a wani gari da ake kira Dammartin-en-Goele, wani karamin gari da ke da mutane 8,000.

'Yan sanda da motocin daukar marasa lafiya sun isa garin da ma motoci masu silke inda ska yi kawanya ga wannan gari da ke da kusanci da filin tashi da saukar jiragen sama na Charles de Gaulle inda wanda ake zargi yayi garkkuwa da wani mutum cikin wani gini a rukunin masana'antu, kamar yanda jami'an 'yan sanda suka bayyana.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Suleiman Babayo