Faransa: Yiwuwar kai harin ta'addanci
May 31, 2016Talla
A cikin wata takardar da ofishin sakataran harakokin wajen Amirka ya fitar kan batun hadarin da ke tattare da yin balaguro a kasashen Turai, ya ce filayen da za a buga wasannin ko kuma wuraren da za a nunasu a Faransa dama a sauran kasashen Turai wurare ne masu hadarin fuskantar hare-haren ta'addancin.
Ofishin sakataran harakokin wajen Amirkar ya gargadi Amirkawa masu tafiya yawon buda ido ko halartar wasu taruka a kasashen na Turai da su kaurace wa shiga wuraren shakatawa da gidajen cin abinci ko manyan shagunan sayar da kaya dama tashoshin sufuri na safa-safa da jiragen kasa. Kazalika Amirka ta ce akwai irin wannan barazana a gasar tsereren kekuna ta Tour de France da Faransar za ta shirya a cikin watan Yuli mai zuwa.