Bude kasuwar Kirsimeti a Faransa
December 14, 2018A ranar Alhamis ce dai minisatan harkokin cikin gidan Faransa Christophe Castaner ya ce tun daga misalin karfe goma sha daya agogon na Faransa wato goma agogon GMT za a tsammaci sake bude kasuwar.
Dan bundugar da ya kai hari a wannan kasuwa a ranar Talata da ta gabata wato Cherif Chekatt, ya bakunci lahira bayan musayar wuta da aka yi tsakaninsa da jami'an tsaro na kasar ta Faransa a ranar Alhamis.
Shi dai maharin dan shekaru 29 wanda dama jami'an tsaro sun san shi da aikata manyan laifuka, sai dai babu na ta'addanci ya bude wuta a kasuwar ta Kirsimeti inda ya halaka mutane uku da wani da wani cikin mawuyacin hali.
Masu gabatar da kara a Faransar dai na duba harin na Talata a matsayin aikin ta'addanci wanda tuni kungiyar IS ke ikirari na da masaniya kansa.