1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa na neman wasu mahara ruwa a jallo

Abdullahi Tanko Bala
May 14, 2024

Yan sanda na neman wasu mahara da suka ce sun yi wa motar jami'an gidan yari kwantar bauna domin kubutar da wani mai laifi da ake tsare da shi.

https://p.dw.com/p/4fr1s
Motar 'yan sandan Faransa
Motar 'yan sandan FaransaHoto: Getty Images/AFP

A kalla Jami'ai biyu na gidan yari a Faransa aka harbe wasu uku kuma suka sami raunuka bayan wani harin kwantar bauna da wasu mahara suka yi wa motarsu 

Hukumomi sun kaddamar da farautar maharan bayan da suka tsere tare da wani mai laifi da ake tsare da shi a gidan yari.

Ministan cikin gida Gerald darmanin ya ce 'yan sanda na iya bakin kokarinsu domin gano maharan.

Ministan shari'a Eric Dupond-Moretti ya ce biyu daga cikin jami'an da suka sami raunuka suna cikin mawyacin hali.

Dupond-Moretti ya ce wannan shi ne karon farko a Faransa tun shekarar 1992 da aka kashe wani jami'in gidan yari yayin da yake bakin aiki.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ci alwashin yin dukkan abin da ya kamata don kama wadanda suka yi wa motar jami'an gidan yarin kwantar bauna.