Faransa: Kutse a takardun Macron | Labarai | DW | 06.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa: Kutse a takardun Macron

Yayin da ya rage sa'o'i kalilan a fara kada kuri'a a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a Faransa, tsakanin Macron da Le Pen, an sake samu kutse ta hanyar Internet na wasu bayanan sirri na yakin neman zaben Macron.

'Yan takarar shugabancin kasar Faransa Marine Le Pen da Emmanuel Macron

'Yan takarar shugabancin kasar Faransa Marine Le Pen da Emmanuel Macron

Cikin wata sanarwa da cibiyar yakin neman zaben dan takarar ta fitar, ta bayyana wannan kutse da cewa na neman kawo rudani ne ga demokradiyyar kasar Faransa kamar yadda ta kasance a zaben shugaban kasar Amirka da ya gabata. Sai dai wallafa bayanan sirrin yakin neman zaben Emmanuel Macron din, a shafin Twiter ke da wuya nan take jam'iyyar Front national ta Marine Le Pen ta sake yada su. Da misalin karfe 12 na daren Jumma'ar da ta gabata ne dai, aka kawo karshen yakin neman zabe a kasar ta Faransa, inda a ranar Lahadi bakwai ga wannan wata na Mayu da muke ciki za a kada kuri'a a zagaye na biyu na zaben.