Emmanuel Macron ya yi sassauci
December 11, 2018Talla
Abin da ya fara kamar zanga-zangar adawa da shirin gwamnati na kara harajin farashin mai dai, ya rikide zuwa gagarumar tarzomar bijirewa shugaban kasar. A jawabin da ya yi wa al'ummar kasar a jiya da maraice, Emmauel Macron ya dauki alhakin wani fanni na halin da kasar ta tsinci kanta a ciki.
Bayan makonni na wannan tashe-tashen hankula, shugaban Faransar ya dauki abin da za a kira mataki na shawo kan wannan tarzoma mafi girma da ya fuskanta tun lokacin da ya dare karagar mulki. A bangaren masu zanga-zangar ta Yello Vest kuwa, tuni suka sanar da kaddamar da sabon gangami a karshen wannan mako da muke ciki. Babu wanda ya san ko matakan na shugaban kasar zai yi tasiri wajen kare sake aukuwar irin wannan tarzoma a fadin Faransar ba.