Faransa da Sahel sun hadu kan yaki da ta′adda | Labarai | DW | 14.01.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa da Sahel sun hadu kan yaki da ta'adda

Faransa da kasashen Sahel biyar ciki har da Jamhuriyar Nijat sun amince da hada karfin soji wajen yaki da ayyukan ta'addanci da ke addabar kasashen. Hakan ya zo bayan taron kolin da suka yi a birnin Pau.

Yayin ganawar da Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi da shugabannin kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar da Moritaniya da kuma Chadi a birnin Pau ra anar Litinin, Faransar ta ce za ta kara yawan sojoji 220. Rundunar hadin gwiwar ta Barkhane bisa amincewar taron na jiya za ta ba da karfi ne iyakoki uku na kasashen tare da taimakon kasashen Turai.    

Shugaba Macron ya ce manufofi biyu masu karfi suka sanya gaba, wadanda suka hada da na soji da na siyasa. Manufar sojin ita ce ta iyakoki uku. Abin da za su fifitawa shi ne yaki da mayakan IS a yankin Sahara, wanda kuma ba zai hana su kaddamar da yaki kan sauran kungiyoyi masu makamai ba.

Mr. Macron ya sami nasarar da yake bukata, musamman samun hadin kan kasashen dangane da ci gaba da kasancewar dakarun Faransa a yankin, abin kuma da al'umomin kasashen biyar ke suka.