Faransa da Afirka na son yakar ta′addanci | Labarai | DW | 15.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa da Afirka na son yakar ta'addanci

Faransa da kasashen Afirka sun hada karfi da karfe a taron da ya gudana a Mali wajen yakar ayyukan ta'addanci da kuma zuwaTurai ta barauniyar hanya.

Kasar Faransa ta hada gwiwa da wasu takawarorinta na Afirka wajen yaki da ayyukan ta'addanci da kuma kwararar bakin haure zuwa Turai ta barauniyar hanya. Shugaba Francois Hollande na Faransa ne ya yi wannan sanarwa bayan taron kolin da ya yi da shugabannin kasashe da gwamnatoci 30 na Afirka a birnin Bamako na Mali.

Ita dai Faransa ta yi alkawarin samar da tallafin raya kasa da habaka tattalin arziki na miliyan dubu 23 na Euro a cikin shekaru biyar masu zuwa ga kasashen Afirka. Tana so ta yi amfani da wannan dama wajen yakar masu fasakorin miyagun kwayoyi da safarar bakin haure da ke zuwa Turai ta barauniyar hanya.