FARA TARON ZABAR SABON FAFAROMA A ROM. | Siyasa | DW | 18.04.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

FARA TARON ZABAR SABON FAFAROMA A ROM.

waliyyan fadar katolika a st Peters Basilica.

default

Kamar yadda kuka ji a labaran duniya,wan nan taro dai an fara shi ne a yau litinin bisa halartar waliyyai 115 daga bangarori daban daban na duniya.

Rahotanni dai sun ashaidar da cewa wadan nan waliyyai 115 zasu kasance ne a cikin dakin santa Marta dake fadar ta batikan,wanda hakan a cewar su hijabine a tsakanin su da wan nan duniya da muke ciki,ba kuma zasu fito ba har sai sun zabi sabon mutumin da zai kasance shugaban darikar ta katolika na 264.

Bayanai dai sun shaidar da cewa a tsawon lokaci da za a dauka a kowace rana waliyyan zasu kada kuriun nasu ne har sau hudu har zuwa lokaci da za a cimma dai daito akan mutumin daya dace ya shugabanci darikar ta katolika.

A dai karshen ko wane zama ana sa ran fitowar hayaki,amma a cewar fadar ta Batikan farin hayaki shine ke nuna cewa an cimma dai daito wajen zabar mutumin daya dace ya shugabanci darikar ta katolika.

Jim kadan kuma bayan fitowar farin hayakin za a kada kararrawa,wanda hakan ke nuni da cewa sabon fafaroma ya samu.

Manya manyan kalubalen da wadan nan waliyyai zasu fuskanta a lokacin wan nan zabe dai shine na banbance banbancen raayoyi game da yankin daya dace a zaso sabon fafaroma da zai gaji marigayi Pope John Paul na biyu.

Bisa wan nan hasashen ne dai ya haifar kowane daya daga cikin waliyyan 115 sai da ya saba laya na cewa ba zai yarda a jirkita raayin sa ba a lokacin wan nan zabe wajen bin son rai ko kuma kama da haka.

Daga dai cikin wadan nan waliyyai 115 guda ashirin sun fito ne daga kasar italiya,kuma daga cikin su akwai mutane 5 wanda ake sa ran za a zabi daya daga cikin su a wa nan sabon mukami.

Wadan nan waliyyai kuwa sun hadar da waliyyi Dionigi tettamanzi da kuma Ak bishop na milan da kuma wanda ya gaje shi wato Carlo Maria Martini da waliyyi na biyu a jerin waliyyain cocin ta batikan wato Angelo Sodano da kuma Camillo Ruini.

Ya zuwa yanzu dai daga cikin wadan nan mutane uku, masu nazarin siyasa ta batikan na ganin cewa Martini ne akan gaba na mutumin da ake hasashew zai kara da dan kasar Jamus din nan wato Joseph Ratzinger,wanda ake kallo a matsayin mutumin dake da kusancin raayi da marigayi Fafaroma John Paul na biyu.

A daya barin kuma an kiyasta cewa kudanci da kuma tsakiyar latin Amurka a yanzu haka nada wakilcin walliyyai 20 daga 115 din. Daga cikin su kuma akwai waliyyai guda shida wadanda ake hasashen ko wane daya daga cikin su ka iya zama sabon fafaroma.

Wadan nan mutane shida sun hadar da Mr Claudio Hummes daga Brazil da Oscar Andres daga Hondurus da Jorge Mario daga Argentina da kuma Dario Castrillon daga Colombia.

Ita ma dai nahiyar Africa a wan nan karon ba a barta a baya ba domin kuwa domin kuwa waliyyi Francis Arinze daga Nigeria na a sahun gaban mutanen da ake sa ran zaba a wan nan sabon mukami.

Daga cikin waliyyai goma kuwa da suka fito daga nahiyar Asia, waliyyi Ivan Dias daga kasar India shine ake gani wanda yafi cancanta a wan nan sabon mukami.

Daga kuwa nahiyar turai akwai waliyyai irin su Joseph Ratzinger daga Jamus da kuma Jean Marie Lustiger daga faransa. Akwai kuma Jose da Cruz daga Lisbon da GodFried Danneels daga Belgium da kuma Christoph daga kasar Austria

A dai lokacin toya wan waina ana sa ran waliyyai daga arewacin Amurka suma zasu taka rawar su wajen ganin an zabe sabon shugaban darikar ta katolika ba tare da daukar dumi ba.

Ibrahim sani.