Falesdinu zata mika wani kudri ga MDD | Labarai | DW | 17.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Falesdinu zata mika wani kudri ga MDD

A wannan Laraba ce, Falesdinawa za su gabatar da kudri a gaban Majalisar Dinkin Duniya na neman kawo karshen mamayar da Isra'ila ke yi musu shekaru da dama.

A ranar Talata ce dai (16.12.2014) mai baiwa shugaban Falesdinawa Mahmoud Abbas shawara Nimr Hammad, ya tabbatar da wannan batu a Ramalla da ke yankin Kogin Jordan, sai dai kuma daya daga cikin jagororin na Falesdinawa a Majalisar Dinkin Duniya, ya sanar cewa a safiyar wannan Larabara ce, za su samu wani zama da wakillan kasashen Larabawa membobi a majalisar domin samun tabbacin goyon bayansu kafin a kai ga mahawara kan wannan batu nan da 'yan kwanaki masu zuwa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu