1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gaza: Shekara guda da dawowar fafutuka

Yusuf Bala Nayaya
March 30, 2019

Dubban Falasdinawa ne ake sa rai za su fito zanga-zanga a iyakar Gaza da Isra'ila a wannan Asabar da ke zama ranar tuni da shekara guda na dawowar zanga-zanga a iyakar ta Gaza da Isra'ila.

https://p.dw.com/p/3FvZr
Palästina Israel Gaza Protetste Verletzte
Hoto: Getty Images/AFP/S. Khatib

An dai ci gaba da zanga-zanga duk mako a fafutukar da Falasdinawa suka sanya a gabansu, ta ganin an dawo masu da yankunan da Isra'ila ta mamaye wadanda ke zama wuraren da iyaye da kakannin Falasdinawan suka zauna, da ma fafutukar ganin an kawo karshen shekaru goma sha biyu na rufe iyakarsu da Isra'ila ta yi.

A wannan Asabar dai ana sa rai na ganin yawan jama'a da za su fita yayin da a bangare guda kuma Falasdinawan ke kiran gudanar da maci na mutane miliyan guda ba kawai a yankin na Falasdinawa ba har da sauran kasashen Larabawa da kasashen Turai.