Falasdinawa na adawa da shirin Trump | Labarai | DW | 26.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Falasdinawa na adawa da shirin Trump

Dubban Falasdinawa sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da shirin Shugaba Trump na sansata rikicin Falasdinawan da Isra'ila ta hanyar samar da tallafin kudi ga Falasdinawa.

Dubban Falasdinawa sun gudanar da zanga-zanga a ranar Talatar nan a yankin zirin Gaza da a biranen Naplouse da Ramallah da Hebron domin nuna adawa da babban taron kasashen duniya da Shugaba Donald trump na Amirka ya kira a Bahrain da nufin shawo kan rikicin Falasdinu da Isra'ila da kuma musamman taimaka wa tattalin arzikin Falasinawa, taron da dama tawagar shugabannin falasdinawan ta kaurace wa a bisa zargin Washington da bangaranci a cikin rikicin.

Shirin Amirkar na ceto tattalin arzikin Falasdinun wanda Jared Kushner ya gabatar na da burin saka jari na kudi biliyan 50 na Dalar Amirka a yankunan Falasdinawa da sauran kasashen larabawa masu makobtaka da ita a cikin shekaru 10.

A shari guda kuma babban taron kasashe aminnan Falasdinu da ya gudana a birnin New York ya samar da tallafin kudi miliyan 110 na Dalar Amirka ga hukumar kula da Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNRWA.