Falasɗinu za ta kafa tutarta a New York | Labarai | DW | 10.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Falasɗinu za ta kafa tutarta a New York

Ƙasar za ta kafa tutarta ne a cibiyar Majalisar Ɗinkin Duniya a wani sabon yunƙurin diplomasiyya domin ganin ƙasar ta samu yanci kai.

Majalisar Ɗinkin Duniya za ta bai wa Falasɗinu izinin kafa tutarta a cibiyar majalisar da ke a New York,a wani sabon mataki na fafutukar diplomasiyya da za ta kai ga amincewar majalisar da ƙasar a matsayin ƙasa mai cikakken yanci.

Nan gaba zuwa da yamma majalisar za ta gabatar da wani ƙudurin na musammun a kan lamarin a taron da za ta yi, wanda kuma bisa ga dukkan alamu ake ganin na cikka suna ne kawai.ko da shi ke ma kawo yanzu ana nuna rashin tabbas a kan matsayin ƙasashen Ƙungiyar Tarrayar Turai masu ra'ayoyi mabanbanta. Amirka da da Isra'ila na yin adawa da wannan ƙudiri kamar yadda suka yi a lokacin da Falasɗinu ta samu matsayin yar kallo a majalisar a shekarun 2012.