1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Somaliya na bukatar agaji inji fafaroma

Abdul-raheem Hassan
August 14, 2022

Fafaroma Francis ya shaidawa dandazon mutane a harabar Vatican cewa yana son jawo hankali ga mummunan rikicin jin kai da ya addabi Somaliya da wasu yankunan kan iyaka.

https://p.dw.com/p/4FW1H
Fafaroma Francis
Hoto: Domenico Stinellis/AP/picture alliance

Shugaban darikar Katolika na duniya Fafaroma Francis, ya zargi yakin Ukraine da karkatar da hankalin duniya daga matsalar yunwar da ake fama da ita a wasu kasashe matalauta. Fafaroman ya yi kiran gaggawa na agajin abinci don dakile matsalar yunwa a Somaliya.

"Ina so in ja hankali game da mummunan matsalar jin kai da ya addabi Somaliya da wasu yankunan da ke kewaye. Al'ummar wannan yanki, wadanda tuni suke rayuwa cikin mawuyacin hali, yanzu sun sami kansu cikin hatsarin mutuwa sakamakon fari. Ina fatan akshen duniya za su amsa kira cikin gagagwa. Abin baƙin ciki shine, yaƙin yana kawar da hankali da albarkatu, amma waɗannan su ne manufofin da ke buƙatar ƙoƙari mafi girma - yaki da yunwa, don lafiya da ilimi."

Hukumar abinci da iikin noma ta Majalisar Dinkin Duniya FAO, ta ce a wannan watan za ta iya shelanta yunwa a hukumance a yankuna takwas na Somaliya a wata mai zuwa idan dabbobi suka ci gaba da mutuwa, farashin kayayyakin masarufi ya kara hauhawa, sannan kuma taimakon jin kai ya kasa kai wa ga wadanda suka fi rauni.