1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafaroma ya soki masu kyamar baki

January 26, 2019

Fafaroma Francis, ya nuna rashin dacewar daukar 'yan gudun hijira a matsayin barazana ta fuskar tsaro, duk da cewar suna tsere wa rigingimu ne.

https://p.dw.com/p/3CEVd
Weltjugendtag Panama 2019 | Papst Franziskus
Hoto: picture-alliance/AP/A. Tarantino

Shugaban darikar Katholika na fadin duniya, Fafaroma Francis, ya ce ba dai dai ba ne a rika daukar 'yan gudun hijira a matsayin da wasu kasashen ke daukarsu na zama barazana ta fuskar tsaro.

A jawabin da ya gabatar a gaban daruruwan dubban matasan darikar lokacin ranar matasa a kasar Panama.

Fafaroma ya shawarci al'umomi ga bukatar karbar duk wadanda ke tserewa daga matsaloli, maimakon sukarsu da ake yi.

Jagoran mabiya darikar ta Katholika na ziyarar kwanaki hudu ne a kasar ta Panama.

Wadannan kalamai ya yi su ne yayin da shugaban Amirka Donald Trump ke ci gaba da kartar kasa wajen ganin sai ya gina ganuwa tsakanin Amirka da kasar Mexico, abin da ya ce na kare mutuncin kasarsa ne.

Fafaroma Francis dai ya ce duk wani da ke kokarin tsananta wa baki, to fa ba Kiristan kwarai bane shi.