1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafaroma Francis: A kawo karshen rikicin Suda

February 18, 2024

Shugaban darikar Katolika na duniya, Fafaroma Francis ya bukaci bangarorin da ba sa ga maciji da juna a Sudan da su kawo karshen fadan watanni 10 a tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/4cY8x
Shugaban Darikar Katolika na Duniya, Fafaroma Francis
Shugaban Darikar Katolika na Duniya, Fafaroma FrancisHoto: GUGLIELMO MANGIAPANE/REUTERS

Alkalumma sun nuna cewa rikicin tsakanin dakarun Sudan da mayakan RSF ya raba dubban mutane da matsuganansu da ma barazanar fari.

A yayin taron addu'o'i a wannan Lahadin, shugaban ya ce fadan ya yi mummunan tasiri ga rayuwar mutane da dama da kuma makomar kasar. Ba a samu nasara ba wajen amfani da hanyoyin diflomasiyya domin kawo karshen yakin basasar.

Fafaroma Francis ya kuma bukaci a kawo karshen rikice-rikicen a wurare irinsu Mozambique da Ukraine da kuma Zirin Gaza, inda a cewarsa; yaki ba ya samar da mafita ba.