Fadar Vatikan za ta karbi ′yan gudun hijira | Labarai | DW | 06.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fadar Vatikan za ta karbi 'yan gudun hijira

Shugaban darikar Katolika na duniya Paparoma Francis ya yi kiran da a tashi tsaye taimakon 'yan gudun hijira kana ya ce Vatikan za ta bada mafaka ga iyalai biya na 'yan gudun hira.

A wannan Lahadin dai 'yan gudun hijirar da ke barin Hungary na cigaba da isa Austria yayin da wasunsu ke wucewa zuwa tarayyar Jamus. Rundunar 'yan sandan Jamus din ta ce yawan wadanda ake zaton za su shiga Jamus din a yau ka iya kaiwa dubu 10.

'Yan gudun hijirar na isa Jamus din ne ta cikin Austria da jiragen kasa inda jama'a ke ke cigaba da tarbarsu da abinci da ruwan sha da kuma kayan sakawa yayin da kungiyoyin bada agaji ke duba lafiyarsu.