1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dubban Falasdinawa na kaurace wa fada a Rafa

May 18, 2024

Ana ci gaba da artabu a kan titunan Rafah, a yayin da Isra'ila ke kara matsa kaimi wajen yakin da take yi da Hamas, lamarin da ya tilasta wa dubban Falasdinawa tserewa.

https://p.dw.com/p/4g29X
Hoto: -/AFP

Sojojin Isra'ila sun bayyana cewa takwarorinsu na sama sun far wa wurare sama da 70 daban-daban a zirin Gaza a yayin da sojojin kasa kuwa ke bi suna neman maboyar Hamas agabashin Rafah abunda suka ce ya kai ga halaka 'ya'yan kungiyar 50 da gano ramukan buyarsu da dama.

Ita kuwa rundunar Hamas mai dauke da makamai ta Al-Qassam Brigades ta ce ta harba rokoki kan birnin Ashkelon na Isra'ila inda ta hari cibiyar rundunar Isra'ilar da ke sansanin 'yan gudun hijira na Jabaila a arewacin Gaza.

Wakilin AFP ya bayyana cewa an zazzaga atilare da makamai masu linzami a gabashin Rafah.