Fada na kara kazanta a Libiya | Siyasa | DW | 28.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Fada na kara kazanta a Libiya

Kasashen ketare na ci gaba da gargadin al'ummarsu da ke Libiya da su gaggauta ficewa, domin kare kansu daga rikicin da ya ke ci gaba da mamaye kasar.i

A yankin gabashin Libiya, sabon fada tsakanin masu tsananin kishin addinin Islama da sojojin kasar ya yi sanadiyyar rayukan mutane 38. Dangane da rigingimu da suka mamaye wannan kasa ta yankin arewacin Afirka ne dai, ya sa hukumomin Jamus da Amirka da Britaniya su ka yi kira ga al'ummansu da su tattara yanasu yanasu su bar kasar.

Amirka dai ta dauki matakai na tsaro domin kare jami'an ofishin jakadancinta na Tripoli da ke kokarin isa Tunisiya da ke makwabtaka. Tafiyar sao'i biyar da mota. Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya yi bayanin dalilansu na kaurar da jami'an na su daga birinin Tripoli;

"Saboda tashe-tashen hankulan masu tayar da kayar baya da ke gudana a Tripoli, musamman da yake a kewayen ofishin jakadanci mu suke faruwa, duk da cewar ba akan ofishin ba ne, yana barazana ga ma'aikatanmu. Dangane da haka ne a yanzu haka muka dakatar da duk wasu ayyuka na diplomasiyya a ofishin na mu, amma ba wai mun rufe ofishin ba ne".

Fada ya kasanta a kewayen ginin ofishin jakadancin na Amirka, inda aka rika harba rokoki da wasu makamai. Matakin janye jami'an Amirkan dai ba zai kasa nasaba da gudun kada a sake fuskantar abun da ya faru a shekaru biyu da suka gabata, lokacin da aka kai wa ofishin jakadancin Amirka da ke Bangazi a yankin arewa maso gabashin Libiya hari, wanda ya yi sanadiyyar rayukan jakadan Amirkan da wasu ma'aikatansa guda uku.

Gwamnati dai bata da wani ikon fada aji, kasancewar masu adawa sun fi yawa, kana tana fuskantar matsalar rashin hukumomin tsaro ingantattu. Wanda ya jagoranceta gargadin yiwuwar ballewar kasar zuwa bangarori daban daban. Sakamakon irin wannan tashin hankali nedai yasa sabuwar majalisar wakilan kasar da aka zaba, ta kaurar matsugunninta daga Tripoli zuwa Bengazi. Sai dai a yanzu haka wani sabon fada ya sake barkewa a wannan yanki, inda masu tsananin kishin addinin islama suka kai hari a sansanin rundunar sojin da ke Bengazi.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin