1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU za ta gana da Poland

November 10, 2021

Firaministan kasar Poland Mateusz Morawiecki zai karbar bakuncin shugaban Majalisar Tarayyar Turai Charles Michel a kan rikicin bakin haure a iyakar Poland da kasar Belarus.

https://p.dw.com/p/42p2y
Grenze Belarus Polen | Migranten-Lager
Hoto: Yuri Shamshur/Tass/dpa/picture alliance/

Ana dai kallon ziyarar na Michel a matsayin nuna goyon baya ga kasar Poland. Tun dai da wasu gungun 'yan cirani suka tunkari iyakar kasashen biyu tare da yunkurin shiga Turai da karfin tuwo, kungiyar EU ta juya baya ga Belarus ta na mai tir da matakin gwamnatin Alexander Lukashenko na ketare huruminsa.

A gefe guda kuma, me yiwuwa Michel ya tursasawa Morawiecki ya amince da taimakon da kungiyar EU zata bayar ga rikicin, wanda amincewar kasar zai bai wa kungiyar damar tura mambobin hukumar kare iyakokinta da kuma rundunar 'yan sandan Turai na Europol. Ko da yake kasar Poland na ikrarin za ta iya magance matsalar kwararowar bakin hauren.

Manazarta dai na ganin Poland na shakkar neman taimako ne saboda rikicin da ke tsakaninta da Brussels kan bin doka da oda a kasar. Kungiyar EU dai ta fusata da gwamnatin Poland mai bin ra'ayin 'yan mazan jiya kan tsawaita da murkushe ayyukan shari''a da kuma rashin mutuntuta hukuncin kotun Tarayyar Turai.