EU za ta dauki mataki a game da batun ba da mafaka | Labarai | DW | 25.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU za ta dauki mataki a game da batun ba da mafaka

Ministocin harkokin cikin gida na kasashe guda 28 na kungiyar EU za su gana a brnin Sofiya domin kaddamar da sauye-sauye na tsarin kungiyar na ba da mafaka.

Bulgarien Jean-Claude Juncker in Sofia (picture alliance/dpa/AA)

Bulgarien Jean-Claude Juncker daya daga cikin shugabannin kungiyar EU

Wannan da ita ce dama ta karshe ta kaddamar da sauye-sauyen wanda EU t nace a kansu, sai dai kuma ta gaza aiwatarwa saboda sabanin da ke a tsakanin kasashen a game da batun kaso na karbar 'yan gudun hijirar. Babu dai tabbas a game da cimma wata matsaya a taron wanda ya kammata a cimma yarjejeniya tsakanin kasashen kafin na da watan Yuni, bayan an kwashe shekara daya da rabi ana neman hanyoyin daidaitawa.