1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU za ta dakatar da sintiri a tekun Baharrum

March 27, 2019

Jiga-jigan kungiyar EU ne dai suka amince da wannan mataki wanda zai fara aiki daga ranar 31 ga watan Maris 2019

https://p.dw.com/p/3FlVK
Europa Symbolbild Grenzschutzmission "Sophia" rettet weniger Menschen
Hoto: picture-alliance/dpa/G. Lami

Shugabannin na EU sun baiyana cewa sintirin jiragen ruwan zai tsaya a karshen wannan watan, amma za a ci gaba da sintiri ta sararin samaniya ta hanyar amfani da jiragen sama da za su rika shawagi don sanya idanu, tare da hadin gwiwar hukumomin kasar Libiya.

Matakin dai bai samu karbuwa dari bisa dari ba daga dukkanin mambobin kungiyar, to amma sun yi baki guda wajne horas da jami'an tsaron gabar ruwan kasa Libiya don samun kyautatuwar shirin.

A cikin watan disamban bara ne dai kungiyar ta amince da takaita shirin mai taken Operation Sophia  a karshen watan Maris. An jiyo yadda mataimakin firministan Italiya Matteo Salvini ke cewa kasarsa ba za ta zama cibiyar jibge 'yan cirani ba, wadanda akasarinsu sun tserewa yake-yake ne da fatara da yunwa daga Afirka da kuma gabas ta tsakiya. Kuma alamu sun nuna cewa Sapain da Faransa da kuma nan Jamus ba su da niyyar sake karbar wasu daga cikinsu, haka ma kasashen Hungary da Poland.

Italien Rettungsschiffe Flüchtlinge
Jirgin ruwan Italiya dauke da 'yan gudun hijiraHoto: picture alliance/AP Photo

Gabar ruwan Alboran da ke tsakanin Spain da Morocco na daga cikin hanyoyin da 'yan ci ranin ke bi wajen tsallakawa turai, tawagar sojin Spain ta jibge runduna guda da ke sa ido a wurin. Laftanar Guillermo Garcia jami'in sojan ruwa ne a kasar Spain mai sa ido kan yadda sintirin ke gudana,

"Mu ne masu bin diddigi domin dakile aniyar masu neman ketare iyaka ba bisa ka'ida ba, ka na muna ceto 'yan ci ranin da ke watagangaririya a kan teku, muna kuma samun tallafin wasu sojojin a yayin aikin namu".

Kyaftin David Cascales direban jirgin sama ne a rundunar sojin Spain.

"Da zarar 'yan ci ranin sun hango jiragenmu na shawagi ko ma dai suka ji alamar muna kusa, su kan nuna duk alama da za a iya hango su, ma'ana su kan daga hannayensu sama da nufin neman agaji".

A bin jira a gani dai shi ne irin matakin da kungiyar tarayyar turan ta EU za ta dauka nan gaba bayan tirjiya daga wasu mabobinta kan takaita wannan shiri da ya zamanto na ceton al'umma da ke gargarar rayuwa.