EU za ta baiwa Turkiya makudan kudade kan ′yan gudun hijira | Labarai | DW | 30.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU za ta baiwa Turkiya makudan kudade kan 'yan gudun hijira

Kungiyar Tarayyar Turai wato EU ta cimma matsaya da kasar Turkiya kan batun rage kwararowar 'yan gudun hijira zuwa nahiyar Turai ta hanyar bayar da taimakon kudi.

Firaministan Turkiya da Shugabar gwamnatin Jamus

Firaministan Turkiya da Shugabar gwamnatin Jamus

Yayin taron da suka gudanar a Brussels na kasar Beljiyam baki dayan bangarorin biyu wato na EU da kuma Turkiya da ke zama hanyar da 'yan gudun hijirar ke bi wajen shiga Turan, sun amince da hada hannu waje guda domin magance matsalar 'yan gudun hijirar.

Kungiyar ta EU dai za ta biya wasu makudan kudade ga 'yan gudun hijirar Siriya miliyan biyu da ke Turkiyan kamar yadda shugaban hukumar Tarayyar Turan Jean-Claude Junker ke cewa:

"Mun shirya bayar da makudan kudi kimanin Euro biliyan uku, inda za a yi amfani da su ta hanyar yin hadin gwiwa da mahukuntan Turkiya."

A jawabin da ya yi Firaministan Turkiya Ahmet Davutoglu ya bayyana cewa lallai wannan rana ce mai dimbin tarihi ga Turkiya kuma za su yi kokarin kare gabar ruwan da 'yan gudun hijirar ke amfani da ita wajen shiga Turai.