EU za ta bai wa Birtaniya lokacin nazari | Labarai | DW | 23.10.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU za ta bai wa Birtaniya lokacin nazari

Shugaban hukumar zartarwar Tarayyar Turai Donald Tusk ya bukaci da a bai wa majalisar dokokin Birtaniyar damar nazari da kuma bayyana matsayinta kan yarjejeniyar da Firaminista Johnson ya cimma da kungiyar.

Tusk ya bukaci shugabannin kungiyar EU da su amince da dage ranar raba gari da Birtaniya domin bai wa 'yan majalisar dokokin Birtaniyar damar nazari da kuma bayyana matsayinsu kan sabuwar yarjejeniyar da Firamnista Boris Johnson ya cimma da kungiyar ta Tarayyar Turai.

Ya bayyana wannan bukata tasa ce a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter inda amma ya ce yana ba da shawarar kungiyar ta EU ta amince da matakin dage ranar raba garin a rubuce kawai ba tare da an sake kiran wani taron koli a kan batun ba.

Kamfanin dillancin larabarn Faransa na AFP ya ruwaito wata majiyar diplomasiyyar mai tushe ta Turai na cewa jakadan kasashen na EU za su gudanar da wani taro a wannan Laraba.Sai dai taron nasu ba na yanke hukunci ba ne, illa dai kawai na neman jin ra'ayin illahirin kasashen kungiyar ne kan ko akwai bukatar daga wa'adin na Brexit ko kuma babu ita

Majalisar dokokin Birtaniya ta amince a bisa manufa da sabuwar yarjejeniyar da Firaminista Boris Johnson ya cimma da shugabannin na EU kan batun raba gari da kungiyar.

Sai dai sun yi watsi da bukatar gwamnatin na ganin majalisar ta bayyana matsayinta ga yarjejeniyar nan zuwa yammacin gobe Alhamis, wa'adin da suka ce  ba zai wadatar ba ga nazarin yarjejeniyar wacce ke kunshe a cikin shafuka 110.