1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar EU ta yi fatali da tsarin Birtaniya

Yusuf Bala Nayaya
September 21, 2018

Shugabanni daga Kungiyar Tarayyar Turai sun yi amfani da taron koli da suka yi a birnin Salzburg na Ostiriya a wannan mako inda suka yi watsi da tsarin na Birtaniya.

https://p.dw.com/p/35J1Z
Theresa May Makes EU Statement
Hoto: Getty Images/J. Taylor

Masu iko daga EU sun yi watsi da tsare-tsaren Firaminista Theresa May ta Birtaniya kan batun da ya shafi tattalin arziki tsakanin bangarorin biyu idan an kammala da shirin ficewar Birtaniya daga Kungiyar EU.

A cewar May dai tsarin da ta zo da shi, shi ne mafita wajen kare huldar kasuwanci da kasashen na Turai idan kasar ta fita daga kawancensu na kasuwanci a kasuwar bai daya, da ma batun da ya shafi jami'an kwastam da hulda da yankin Ireland. Sai dai daga bangaren na shugabanni a Kungiyar EU sun nunar da cewa tsarin na May zai iya zama barazana ga kudirin kasuwar bai daya da suke da ita tsakanin kasashensu.