EU ta yabawa yan sandan Jamus a G20 | Labarai | DW | 10.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU ta yabawa yan sandan Jamus a G20

'Yan sandan Jamus sun taka rawar gani wajen shawo kan tarzoma a taron G20 a Hamburg a cewar shugaban hukumar tarayyar turai Jean-Claude Juncker

G20 Gipfel in Hamburg | Polizei (Reuters/P. Kopczynski)

Yan sandan Jamus cikin shirin ko ta kwana

Shugaban hukumar tarayyar Turai Jean-Claude Juncker a yau Litinin ya kare matakin da yan sandan Jamus suka dauka a yayin zanga zangar lumana da ta rikide zuwa tarzoma a taron kungiyar kasashe ashirin masu cigaban masana#antu na duniya da aka kammala a birnin Hamburg a nan Jamus.

A cikin wata sanarwa Juncker yace rashin adalci ne sukar lamirin da ake yi wa yan sanda akan yadda suka tunkari lamarin.

Yace yan sanda sun sadaukar da rayuwarsu a wannan aiki mawuyaci, yana mai cewa sun cancanci yabo ne amma ba suka ba.