EU ta tallafa wa kasashen G5 Sahel da kudi | Labarai | DW | 29.04.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU ta tallafa wa kasashen G5 Sahel da kudi

Kungiyar tarayyar Turai ta bayar da tallafin kudi miliyan 194 na Euro ga kasashe mambobin kungiyar G5 Sahel domin samar da kayan aiki ga sojojin kasashen a ci gaba da yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda

Kungiyar tarayyar Turai ta bayar da tallafin kudi miliyan 194 na Euro ga kasashe mambobin kungiyar G5 Sahel domin samar da kayan aiki ga sojojin kasashen a ci gaba da yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda musamman a kan iyakar da ta hada kasashen Mali Nijar da Burkina Faso inda matsalar ta'addancin ta fi kamari.

 Shugaban Hukumar koli ta tarayyar Turan Charles Michel ne ya sanar da hakana agaban manema labarai a karshen taron da ya gudanar ta kafar Intanet da shugabannin kasashen biyar na Mali, Nijar, Burkina Faso, Moritaniya da Chadi a yammacin jiya Talata.

 Kazalika kungiyar ta EU ta dauki alkawarin sake nazarin bukatar da kasashen na G5 Sahel suka shigar a gabanta ta ganin kungiyar ta EU ta yafe masu baki daya kudaden bashin da take bin su domin taimaka masu ga rage wahalar kudaden da suka zuba a fannin yaki da annobar Coronavirus a kasashensu.