1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan takarar shugaba da takunkumin EU

Yusuf Bala Nayaya
December 10, 2018

Kungiyar Tarayyar Turai ta kara takunkumi ga dan takarar shugabancin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da ke samun goyon bayan Shugaba Joseph Kabila tare da wasu 'yan kasar 13, makonni biyu kafin zaben shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/39oYG
Kongo Emmanuel Ramazani Shadary
Hoto: REUTERS

Bayan shekaru biyu da aka dauka ana samun tsaiko a zaben shugaban kasa da 'yan majalisa da shugabannin kananan hukumomi a kasar ta Kwango mai arzikin albarkatun kasa, daga karshe an tsara zaben a ranar 23 ga watan nan na Disamba. Zaben da Emmanuel Ramazani Shadary da ke samun goyon baya na Kabila da ya mulki kasar tun 2001 zai fafata da bangaren adawa. Sai dai Shadary na takarar zaben shugabancin na Kwango bayan da Kungiyar EU ta kara tsawaita takunkumi da aka kakaba masa da ya shafi hana tafiye-tafiye da hana shi taba kadarorinsa na waje, takunkumin da aka kakaba masa sa'ilin da yake ministan harkokin cikin gida, saboda hannunsa a afka wa gangamin 'yan adawa.