EU ta ba da tallafi ga kasashen Yankin Sahel | Siyasa | DW | 06.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

EU ta ba da tallafi ga kasashen Yankin Sahel

Kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da tallafi na kukade Euro miliyan 50 ga kungiyar kasashen yankin Sahel su biyar domin yaki da ta'addanci ta hanyar kafa wata rundunar soji ta hadin gwiwa.

Wannan runduna ta hadin gwiwa dai za ta kula da yin aikin saka ido a yankin na Sahel dangane da hare-haren da 'yan ta'adda suke kai wa. Tun a cikin watan Fabrairu da ya gabata aka kaddamar da tsarin kafa wannan runduna ta hadin gwiwa ta kasashen G5 Sahel. Sakamakon ta'azzarar harkokin ta'addanci ne dai a yankin Sahel, kasashen yankin guda biyar da suka hada da Mali da Nijar, da Burkina Faso da Chadi da kuma  Mauritaniya, suka samar da wani tsari na hadin gwiwa da zai ba su damar saka ido da kuma yakar  ta'addanci. Kuma hakan ya samu tallafin kudi daga Kungiyar Tarayyar Turai na Euro miliyan 50 domin  ganin wannan runduna ta hadin gwiwa ta soma aiki nan da zuwa karshen wannan shekara.

Babbar ayar tambayar da jama'a ke azawa a yanzu shi ne yaya wannan runduna za ta yi aiki kuma na wa ne addadin sojojin da za ta kunsa. Nicolas Desgrais masani ne na Yankin Sahel.

 Ya ce: ''Mafi yawan sojoji na kasashen Yankin na Sahel kamar sauran ‘yan uwansu na sauran kasashen nahiyar Afirka, na fama da karancin kayayyakin aiki. Suna bukatar motoci, da jirage masu saukar ungulu, da ma jiragen yaki, sannan da cibiyoyi na bayar da horo na zamani, tare da samun dakaru na musamman da za su kasance a cikin barikokin sojoji masu cikakken tsaro. A yanzu haka wadannan kasashe na dogaro ne da Tarayyar Turai, musamman da kasar Faransa.''

Sauti da bidiyo akan labarin