EU: Shakku kan yarjejeniyar ′yan gudun hijira | Labarai | DW | 29.06.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU: Shakku kan yarjejeniyar 'yan gudun hijira

Wasu kasashen Turai sun fara nuna shakkunsu a game da yiwuwar mutunta yarjejeniyar da kasashen Turai suka cimma a daren jiya kan batun 'yan gudun hijira a taron koli na birnin Brussels.

Wasu kasashen Turai sun fara nuna shakkunsu a game da yiwuwar mutunta yarjejeniyar da kasashen Turai suka cimma a daren jiya kan batun 'yan gudun hijira a taron koli na birnin Brussels, yarjejeniyar da ta tanadi kafa wasu cibiyoyin karbar 'yan gudun hijira a wasu kasashen da ba na Turai ba da kuma dora wa ko wata kasa wani kaso na kudin tallafin da ya kamata ta bai wa wasu kasashen Turan kamar su Italiya domin daukar dawainiyar 'yan gudun hijirar. Yanzu haka dai kasashe kamar su Poland da Hangari da Jamhuriyar Chek da Slovakiya sun ki su ba da hadin kansu ga shirin suna masu nacewa a kan ganin an yi watsi da matakin cilasta wa kowace kasar Turai ba da wani kaso na kudin daukar nauyin 'yan gudun hijirar. A taron kolin kasashen Turan na jya dai kasar Italiya ta yi barazanar ficewa daga taron matsawar kasashen Turan suka ki amincewa da shirin tallafa wa kasashen Turan da ke kasancewa kofofin shigowar 'yan gudun hijirar.

Kungiyar likitocin na gari na kowa ta Medecins sans Frontieres ta soki lamirin yarjejeniyar da kasashen Turai suka cimma kan batun 'yan gudun hijira tana mai cewa daga yanzu su ke da alhakin duk mutuwar wani dan gudun hijira da za a samu a nan gaba.