EU: Sabbin manufofi kan 'yan gudun hijira
May 14, 2024Talla
Ministocin tattalin arziki daga kasashe 27 na kungiyar tarayyar Turai sun amince da bukatar yin garanbawul ga manufofin kungiyar kan 'yan gudun hijira da masu neman mafaka.
Shirin ya bukaci tsaurara matakai a kan iyakoki da kuma raba hidimar daukar nauyin masu neman mafaka a tsakanin mambobin kasashen Turan.
Garanbawul din da zai kunshi gyaran sassan dokoki guda goma ya sami amincewar galibin kasashen kungiyar ta EU duk da turjiyar da kasashen Hungary da Poland suka nuna.
Sabbin dokokin za su fara aiki ne daga shekarar 2026.