EU: Karin wa'adin dokar takaita tafiye-tafiye
May 8, 2020Talla
A tsakiyar watan Maris na bana ne kasashen 27 na kungiyar Tarayyar Turan suka amince da rufe iyakokinsu daga duk wasu harkoki na shige da fice da ba su da wani mahimmamci a yanzu a kokarin takaita yaduwar wannan annoba ta COVID-19 da duniya ke fama da ita.
Kwamishiniyar harkokin cikin gida a kungiyar Ylva Johansson, ta ce kungiyar ta EU za ta bude iyakokinta muddin al'amura suka sasauto, wanda dama dai babu wani shinge na shige da ficen a tsakanin kasashen kungiyar da ake kira Schengen.