1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU za ta tallafa wa kasar Lebanon

Abdoulaye Mamane Amadou
August 7, 2020

Kungiyar Taraayar Turai ta ce za ta halarci taron koli da masu hannu da shuni ke shirin gudanarwa karkashin jagorancin Faransa da niyar samar da kayayyakin agaji ga kasar Lebanon.

https://p.dw.com/p/3gcdp
Außerordentliche Plenarsitzung des EU-Parlaments in Brüssel
Hoto: Reuters/F. Walschaerts

Kungiyar EU ta ce ta na goyon bayan taron gidauniyar tattara kudade don tallafi ga jama'ar da iftila'in fashewar wasu ababe ya shafa a da ya hallaka akalla mutane 150, wasu kimanin 5000 kuma suka ji rauni.

Tuni shugaban hukumar zartawar kungiyar ta EU Charles Michel ya bayyana anniyarsa ta kai ziyarar aiki a birnin Beyrouth a ranar Asabar, domin nuna alhinin daukacin tarayyar Turai ga al'ummar Lebanon, inda zai gana da shugaba Michel Aoun da wasu kusoshin gwamnatin kasar.

Tuni EU ta ware Euro miliyan 33 a matsayin zangon farko na agajin gagawa ga kasar, tare da saka baki ga sauran kasashen nahiyar don kawo nasu dauki ciki gagawa.