EU da Kanada sun ratabba hannu kan CETA
October 30, 2016Talla
Firaministan kasar Kanada Justin Trudeau ya gana da shugabanni daga Kungiyar Tarayyar Turai ta EU a ranar Lahadin nan inda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kasuwanci da ake wa lakabi da CETA, da za ta yi tasiri ga mutane miliyan 500 daga Turai da miliyan 35 daga Kanada.
Shugaban majalisar Tarayyar Turai Martin Schulz ya bayyana cewa wannan rana ce mai muhimmanci ga Turai da kuma Kanada.
"Ina ganin wannan rana ce mai alfanu ga Kungiyar Tarayyar Turai da Kanada bayan lokaci mai tsawo a wannan rana mun rattaba hannu kan yarjejeniya mai tsari na kasa da kasa, abin da zai amfani al'ummarmu a nan gaba wasu ma su yi koyi."