EU da ECOWAS na son zabe mai tsabta a Najeriya | Siyasa | DW | 17.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

EU da ECOWAS na son zabe mai tsabta a Najeriya

Wakilan kungiyar Tarayyar Turai da da ma kungiyar ECOWAS sun gana da shugaba Goodluck Jonathan dan jaddada bukatar yin zabe mai tsabta da nagarta

Kasa da tsawon makonni shida da komawa fagen fama da nufin kaiwa ga zabuka karbabbu, daga dukkan alamu har yanzu akwai sauran rina cikin kaba duk da tabbacin mahukuntan kasar na tabbatar da komai dai dai. Hankula dai sun tashi rayuka sun yi baki cikin kasar da ta tsara zabuka amma ta daga a wani abun da ya kai ga damuwa da ma samar da fassara iri-iri ciki da ma wajen kasar da ra'ayi ya rabe kama daga tsohon shugaban kasar da ya zargi gwamnatin da neman zarcewa kan mulki ko ta halin kaka, ya zuwa masu adawar da suke zargi da kokari na binne su da rai.

Martanin kungiyar EU dangane da zabe

Su kansu masu kallon zaben na waje dai sun shiga dardar da damuwa sakamakon alamun dada lalacewar da take yi ga kasar da shugabanninta ke kara tabbacin yin gyara amma kuma al'amura ke dada rudewa yanzu. Mr Santiago Fisas dai na zaman babban jami'in da Tarrayar Turan ta EU ta turo cikin kasar don kallon zaben. Mutumin kuma da ya jagoranci ganawa da shugaban kasar da nufin ji daga bakinsa bisa jerin rudanin.

“ Ina farin ciki da tabbacin da shugaban kasa ya ba mu bisa tabbatar da rantsar da sabuwar gwamnati a ranar 29 ga atan Mayun da ke tafe. na jin wannan labari ne mai dadi domin wannan yana cikin kundin tsarin mulki. Bani da shakkun zai yi haka saboda shi ne shugaban kasa kuma ya baiyanna haka a bainar jama'a. Mu ma kuma ya shaida mana. Na tambaye shi ko batun tsaro na iya jawo matsala kan zaben amma yace baya ji ko da ba kai karshe ba to kuwa za'aci karfinsa kwarai”

ECOWAS ma ta damu da shirye-shiryen zaben Najeriya

To sai dai kuma ko bayan turawan dai, suma makwabtan kasar ta Najeriya na kara nuna damuwa ga shirin zaben da ya kai ga hukumar yankin yammacin Africa ta ECOWAS kaddamar da bincike a bisa shirin tare da mika rahoton nasu ga masu ruwa da tsaki da harkoki na zabe da siyasa cikin kasar.

Sauti da bidiyo akan labarin