EU da Birtaniya na takun saka tsakaninsu
September 10, 2020Kungiyar Tarayyar Turai ta dibar wa Birtaniya har zuwa karshen wata Staumba don ta janye kudirinta na soke wani bangare na yarjejeniyar rabuwa da juna na Brexit idan tana son kanta da lafiya. Wannan wa'adin ya biyo bayan wani taro a Landan da EU ta kira cikin gaggawa da nufin samun karin haske kan aniyar Birtaniya na kin mutunta abin da suke cimma tun watanni taran da suka gabata.
Mataimakin Shugaban Hukumar zartaswa na EU Maros Sefcovic ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga gwamnatin Birtaniya da ta janye kudirin dokar , Sannan ya jaddada cewa EU ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen klubalantar Birtaniya a kotun Turai ba.
Sai dai a lokacin da yake maida martani, karamin ministan Birtaniya Michael Gove ya yi watsi da wa'adin na EU, inda ya ce gwamnatin Birtaniya za ta ci gaba da bin kudirin na soke wasu tanade-tanade na yarjejeniyar ta Brexit.
Wannan rikicin na faruwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Birtaniyya ke ci gaba da zaman tattaunawa da EU kan dangantakar bangarorin biyu bayan raba gari kwata-kwata tsakaninsu.