1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU: Akwai bukatar gyara a tsarin zaben Najeriya

March 11, 2019

'Yan Kungiyar EU da suka sanya idanu kan zaben gwamnoni a Najerya sun ce akwai akwai bukatar yin gyaran fuska a daukacin tsarin zaben Najeriya.

https://p.dw.com/p/3Eolo
Nigeria Präsidentschaftswahlen Schlange vor Wahllokal
Hoto: Getty Images/AFP/L. Tato

'Yan kallon na Kungiyar EU 73 ne dai suka sanya idanu kan zabukan da aka gudanar a kasar musamman ma na gwamnonin da aka yi a ranar Asabar din da ta gabata a wasu daga cikin jihohin kasar. A cikin wani rahoto na wucin gadi dai sun ce tsarin ya na bukatar gyara a matakai daban-daban in ha ana da bukatar samun inganci a zanen na Najeriya.

Masu sa idon dai sun ce duk da cewar akwai cigaba a cikin gudanarwar zaben idan aka kwatanta shi da abinda ya faru a na shugaban kasa da ya wakana makonni biyun da suka gabata, matsalar rashin tsaro da aka samu ta dusashe cigaban sannan an yi amfani da kujerar mulki ta hanyar da ba ta dace ba, baya fa gazawar da suka ce an samu daga cibiyoyin da ke da ruwa da tsaki da batun zaben.

Wani abu har wa yau da 'yan kaon zaben na Najeriya suka tabo shi ne asarar rayuka da aka samu inda ta ce ya kyautu a hukunta wadanda ke da hannu wajen zubar da jini da aka samu. Baya ga wannan batu kuma, zaben ya kuma fuskanci rashin fitar jama'a sai dai duk da wannan, a share guda masu sa idon sun yaba an yadda aka bude rumfunan zaben a kan kari da kuma yadda aka yi kidayar sakamakon a bainar jama'a.