1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben majalisa a kasar Ethiopiya

Daniel Pelz ZMA
June 21, 2021

Sai dai zaben ba zai gudana a kusan kashi daya cikin biyar na kasar ba saboda matsalolin kayan aiki ko tashin hankali. Wannan ya hada da yankin Tigray da ke fama da rikici a arewacin Ethiopiya.

https://p.dw.com/p/3vHlS
Parlamentswahl in Äthiopien
Masu kada kuri'u a EthiopiyaHoto: S. Wegayehu/DW

 

A wannan Litinin din ce ake gudanar da zaben 'yan majalisa a kasar Ethiopiya, wanda ya zo kwanaki kalilan bayan da mahukunta suka sanya sabbin dokoki ga jam'iyyun siyasa da kuma kafafen yada labarai game da zabe. Yayin da a daya hannun kuma kanfanin Facebook ya cire wasu shafukan boge da aka danganta su da gwamnatin ta Ethiopiya.

Hukumar zaben kasar ta Ethiopiya ta hana gudanar da gangamin yakin neman zabe kwanaki biyar kafin ranar kada kuri'a tare da gindaya sabbin dokoki ga kafafen watsa labarai na cikin gida. A cikin wata sanarwa da ta watsa a shafinta na Facebook, hukumar ta ce  kafofin yada labarai ba su da 'yancin watsa kowane irin abu da ya shafi zabe, ciki har da yin hira da 'yan takarar jam'iyyun siyasa. Sai dai mai magana da yawun hukumar zaben kasar Soleyana Shimeles ta ce ba a fitar da wannan tsari don hana kafofin watsa labarai rawar gaban hantsi ba, a'a, amma an yi shi ne don mayar da hankali kan ilimantar da al'umma kan muhimman kada kuri'a.

" Abinda muke maida hankali shi ne sanar da masu kada kuri'a game da yadda ake kada kuri'a, game da takardun jefa kuri'a, game da yadda za su iya kada kuri'a da kuma abin da ya kamata su yi a ranar zabe. Muna kira ga kowa da kowa har da jam'iyyun siyasa da kafofin watsa labarai da su maida hankali a kan wadannan matakai,  kuma a ba wa masu jefa kuri'a bayanai game da ranar zabe da kuma yadda za su iya jefa kuri'unsu. Bayan haka za mu je ga batun sakamakon. Don haka kwanakin nan sun shafi ilimimantar da masu jefa kuri'a ne, da kuma aikin samar da kayan zabe da kula da jigilarsu. "

Äthiopien Wahl 2021 | Wahllokal Addis Abeba
Masu zabe a Addis AbebaHoto: Ben Curtis/AP Photo/picture alliance

Sai dai wasu 'yan jarida na Ethiopiya na ganin cewa sabbin ka'idojin sun yin mummunan tasiri ga labaran da suke gabatarwa gabanin zaben. Neamin Ashenafi, Mataimakin babban editan a jaridar The Reporter da ke da mazauninta a birnin Addis Ababa na daga cikin masu wannan ra'ayi.

"Wannan matakin na jawo komabaya. Yana shafar kwararar bayanai tsakanin jam'iyyun siyasa da cibiyoyin yada labarai. Ni kaina na shaida haka, yana takaita ayyukanmu, da mu'amalarmu da jam'iyyun siyasa na adawa, . Wannan ya sanya wani shinge tsakanin masu jefa kuri'a, kafofin watsa labarai da 'yan siyasa. "

Karin bayani: Ethiopiya: Zaben yanki a Tigray

Kungiyar kare hakkin 'yan jarida ta kasa da kasa Reporters without Border (RSF) ita ma ta nuna damuwa dangane da wannan mataki. Shugaban RSF na Afirka, Arnaud Froger, ya fada daga Paris cewa haramci hana gangamin zabe na kwanaki biyar ya yi yawa.

"Ana shaida da irin wannan lokacin na dakatar da gangamin yakin neman zabe ga jam'iyyun siyasa ko kuma kafofin watsa labarai daidai lokacin zabe. Amma a yawancin kasashe, sa'o'i 24 ko 48 ne kawai. Wadannan kwanaki biyar lokaci ne mai tsawo sosai ga mutane su dakatar da takurawa kuma su daina tattauna batutuwan da suka shafi zabe. "

Karin bayani:  An kama 'yan adawa a kasar Habasha

'Yancin yada labarai ya bunkasa sosai a shekarar 2018 bayan da firaminista mai ci Abiy Ahmed ya hau kan mulki, inda ya ba da umarnin sakin ‘yan jaridar da ke daure tare da ba da damar kafafen yada labaran da gwamnatin da ta gabata ta hana damar ci gaba da aikinsu. Amma kungiyar Reporters without Border ta ce lamarin ya sake ta'azzara, inda suka bayar da misali da kame 'yan jarida ba bisa ka'ida ba a karshen shekarar 2020 da kuma korar wakilin jaridar New York Times a watan Mayu.

Kasar Habasha tana sahun na 101 daga cikin kasashe 180 da ke mutunta ‘yancin‘ yan Jaridu a shekarar 2021.

Parlamentswahl in Äthiopien 2021
Zaben 'yan majalisa EthiopiyaHoto: S.Getu/DW

Dama a ranar Alhamis, kanfanin Facebook ya ba da sanarwar soke shafuka Facebook 65, da na Instagram 32 saboda abin da ya kira "halayyar rashin dabi'ar kwarai." A cewar wata sanarwar Facebook, wadannan sakonnin da aka wallafa da harshen Amharic sun kunshi abubuwan da  Firayiminista Abiy Ahmed da Jam'iyyar da ke mulki ke gudanarwa, tare da sanya sharhi mai sukar 'yan siyasa da kungiyoyi daban-daban na adawa a Habasha, ciki har da 'yan gagwarmayar Oromo, da kungiyar' neamn 'Yancin yankin Tigrai da sauransu.

Karin bayani: Demokradiyyar Ethiopiya na cikin barazana

Facebook ya zargi hukumar leken asiri  ta kasar, da Hukumar Sadarwa ta Ethiopia da aikata wannan danyen aiki.

Oliver Lindow, Kwararre kan 'yancin fadan albarkancin baki a kafar intanet  ya ce ya yi imanin cewa yakin neman zabe Ethiopiya ya yi matukar tasiri wajen soke shafukan.

"Wadannan shafuka suna da mabiya 766.000. Wannan yana nufin cewa suna da kyakkyawar hanyar yada manufofinsu. Kuma idan aka yi la'akari da cewa mabiya za su yi sharing abubuwan da aka wallafa, kuma ana aliking, to tabbas za ku iya jirkita ra'ayoyin mutane."

Tun farko dai, an tsara gudanar da zaben 'yan majalisa a Ethiopian ne a watan Agusta 2020 amma aka dage shi sakamakon annobar COVID.