Habasha ta kama 'yan adawa
July 6, 2020Talla
Shugaban jam'iyyar nan mai fafatukar samun 'yancin Oromo ta (OLF) Dawud Ibsa ya bayyana cewa duk da kama kusoshin jam'iyyar har kawo yanzu ba a bayyana wasu muhimman dalilan da suka sa aka kama membobin jam'iyyar ba.
A makon da ya gabata ne rikici ya barke a babban birnin kasar ta Habasha wato Addis Ababa da yankin Oromiya, sakamakon mutuwar mawaki Hachalu Hundessa dan kabilar Oromo, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 156 ciki har da jami'an 'yan sanda 11, baya ga wasu akalla 170 da suka jikkata a yayin tashin hankalin, wanda ke zaman mafi tsanani tun bayan darewar firaminsitan kasar Abiy Ahmed kan madafun iko.