Erdogan ya halarci taron gangami kan yaki da ta'addanci
September 20, 2015Talla
Shugaban ƙasar da sauran jama'a da suka hallara a wannan Lahadin a dandali na Yenikapi, sun yi Allah wadai da aiyyukan ta'addanci na 'yan tawayen Ƙurdawa a wannan ƙasa. Cikin jawabin da ya yi a gaban dubban jama'a, Shugaba Erdogan ya ce "babu maganar nuna wani sassauci ga 'aiyyukan ta'addanci". Haɗin gwiwar ƙungiyoyi masu zaman kansu ne dai suka kira wannan taron gangamin a filin na Yenikapi, wani babban fili da ka iya ɗaukan aƙalla mutane milian ɗaya da rabi.
Sai dai tuni ake ganin wannan taron gangamin na mai kama da yaƙin neman zaɓe, ganin cewar watanni shidda ne suka rage ga zaɓen 'yan majalisun dokokin ƙasar na kafin lokaci, wanda shugaban ya kira bayan da aka kasa samun daidaito wajen kafa gwamnatin haɗaka a wannan ƙasa.