1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bai wa shugaban kasar Faransa lambar yabo

Abdourahamane Hassane
May 10, 2018

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya samu kyautar lambar yabo ta girma da aka bashi a birnin Aachen na Jamus.

https://p.dw.com/p/2xUjE
Verleihung Internationaler Karlspreis an Macron
Hoto: Getty Images/AFP/P. Stollarz

Shugaban na Faransa ya samu kyautar lambar yabon ne a birnin Aachen saboda manufofinsa na samu hadin kai na kasashen Turai. Wannan lambar yabo da birnin na Aachen ke bayar da ita tun a shekara ta 1950 ga gwarzayen mutane da suke fafutuka don nahiyar Turai. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta taba samun kyautar  a shekara ta 2008.