EgyptAir: An fara gano wasu sassan jikin dan Adam | Labarai | DW | 20.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EgyptAir: An fara gano wasu sassan jikin dan Adam

Ministan tsaro na Girka Panos Kammenos ya ce ya samu bayanai daga mahukuntan na Masar cewa sun ga wani bangare na jikin dan Adam ban da tarkace na jirgi.

Dakarun sojan ruwan Masar da na sama sun gano wani bangare na jikin dan Adam da wasu kayayyaki da suka hadar da jakankkuna da tarkace na jirgin EgyptAir mai lamba 804 wanda ya fadi da fasinjoji 66 a lokacin da ya baro birnin Paris kan hanyarsa ta zuwa birnin Alkahira na Masar kamar yadda ma'aikatar tsaro ta Masar da Girka suka bayyana a ranar Jumma'an nan.Ministan tsaro na kasar Girka Panos Kammenos ya ce ya samu bayanai daga mahukuntan na Masar cewa sun ga wani bangare na jikin dan Adam banda tarkace na jirgi da kayayyaki na mutane a yankin da suke gudanar da bincike a Tekun Meditareniya.

Birgediya Janar Mohammed Samir da ke magana da yawun sojan na Masar ya bayyana a shafinsa na Facebook cewar an samu takarcen jirgin a cikin teku daga nisan kilomita 290 Arewa daga gabar teku daga birnin Alexandria. Kasashen da suka shiga aikin binciken dai sun hadar da Faransa da Girka da Italiya da Cyprus da Birtaniya kamar yadda ma'aikatar tsaron ta Masar ta bayyana.