1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

ECOWAS ta kakaba wa Mali takunkuman tattalin arziki

January 10, 2022

Kasashen yammacin Afirka, sun yanke shawarar kakaba wa Mali karin takunkuman tattalin arziki saboda janye zaben watan Fabrairu da sojojin juyin mulki suka yi.

https://p.dw.com/p/45KmE
Ghana Accra | Economic Community of West African States | ECOWAS
Hoto: IVORY COAST PRESIDENTIAL PRESS SERVICE/REUTERS

Kasashen sun ce za su tsananta wa Malin ne ta fuskatar rufe iyakoki da ma haramta cinikayya a tsakaninsu.

Kungiyar raya tattalin arzikin yankin yammacin na Afirka ECOWAS ce ta yanke wannan shawara a taronta na koli da aka yi a Ghana.

Za ma a yanke duk wani abu mai nasaba da tallafin kudade ga Malin, da ma rufe asusunta a babban bankin kasashen ECOWAS.

Jagororin gwamnatin Mali a Bamako, sun ce zabe a Mali sai bayan shekaru hudu nan gaba, sabanin watan Fabrairu da suka amince da fari.