ECOWAS ta jinkirta hambarar da Jammeh | Labarai | DW | 20.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

ECOWAS ta jinkirta hambarar da Jammeh

Kungiyar ECOWAS ko CEDAO ta sake bai wa Yahya Jammeh damar karshe ta nema mafaka a ketare ko kuma sojojinta su saukeshi da tsinin bindiga bayan da wa'adinsa mulkinsa a kare a Gambiya.

Shugabanin ECOWAS ko CEDEAO sun jinkirta shirinsu na amfani da karfi wajen hambarar da Yahya Jammeh daga mulkin Gambiya domin bashi damar gudun hijira a wata kasa. Shugaban Guinea Alpha Conde ne ke kokarin shawo kanshi don ya nemi mafaka a ketare. Dama a wannan Jumma'ar ce wa'adin da kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO ta dibar wa Jammeh na barin mulki cikin girma da arziki ko kuma sojojinta su far masa ke karewa.

Shi dai Yahya Jammeh wanda ya dare kan karagar mulkin tun shekarar 1994, ya na nema kotun tsarin mulkin kasarsa ta yi nazarin karar kalubalantar zabe da ya shigar kafin ya sauka. Sai dai kuma kasashen yammacin Afirka suna matsa masa lamba domin ya mutunta sakamakon da hukumar zaben kasar ta bayar, inda ta nunar da cewa ya sha kaye.

Kasashe biyar da suka hada da Najeriya da Senegal da Ghana da Togo da Mali sun tura da sojoji dubu bakwai zuwa Gambiya don saukar da Yayha Jammeh da tsinin bindiga. Tuni ma Majalisar Dinkin Duniya ta albarkanci wanna mataki.