1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

ECOWAS ta gargadi Mali a kan korar jakadanta

October 28, 2021

Kungiyar ECOWAS ta nuna rashin jin dadi da korar jami'inta da gwamnatin tayi a Mali, matakin da ta ce ya zarta abin da hankali zai dauka. Tun a bara ne Mali ke fama da rikici.

https://p.dw.com/p/42JdE
ECOWAS Westafrikanische Staaten verhängen Sanktionen gegen Mali und Guinea
Hoto: Nipah Dennis/AFP

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, ECOWAS, ta sha alwashin ci gaba da matsa wa Mali lamba har sai kasar ta koma ga tsarin mulki irin na dimukuradiyya.

ECOWAS wadda ta fusata da matakin gwamnatin soja a Mali na korar jakadanta da ke kasar, ta ce abin da Malin ta yi ya yi tsauri.

A ranar Litinin ne da ta gabata ne, gwamnatin soja da Kanal Assimi Goita ke jagoranta, ta bai wa Hamidou Boly, wakilin na ECOWAS wa'adin sa'o'i 72 da ya bar kasar.

Ministan harkokin wajen Malin, Abdoulaye Diop, ya zargi wakilin na ECOWAS da hulda da kungiyoyin da ke harkokin da suka ci karo da manufofin gwamnati.

Cikin watan Agustan bara ne dai Mali ta fada cikin rigimar siyasa, da ta kai ga hambare gwamnati Shugaba Ibrahim Boubacar Keita.