1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS na neman sansanta rikicin Guinea

Mouhamadou Awal Balarabe
March 16, 2020

Shugaba Issoufou na Nijar da takwaransa Buhari na Najeriya za su je Guinea don nazarin rikicin siyasa da ake fama da shi a kasar tun watannin baya sakamakon zargin shugaba Alpha Conde da neman yin tazarce.

https://p.dw.com/p/3ZXoW
Niger Mahamadou Issoufou und Muhammadu Buhari
Hoto: DW/S. Boukari

Wata tawagar shugabannin kasashen Afirka ta yamma hudu hudu za ta ziyarci Conakry babban birnin Guinea a ranar Talata domin neman warware rikicin siyasa da ya kunno kai sakamakon kuri'ar raba gardama kan sabon kundin tsarin mulki da ake shirin gudanarwa. Fadar shugaban kasar Côte d'ivoire ce ta tabbatar da wannan labarin, inda ta ce Mahamadu Issoufou na Nijar da Muhammadu Buhari na Najeriya za su kasance cikin tawagar baya ga Nana akufo-Addo na Ghana da kuma Alassane Ouattare na Côte d' Ivoire.

Duk da jinkirta zaben 'yan majalisa da zaben raba gardama da gwamnatin Guinea ta yi, takaddama da zargi daga kasashen duniya sun ci gaba da wakana kan sahihancin shirin zaben. Kungiyar kasashe rainon Faransa ta la Francophine da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta Afirka ta Yamma sun nemi hukumomin Guinea za su janye sunayen mutane miliyan 2.5 daga kundin masu kada kuri'a idan suna son zaben ya samu karbuwa.

Akalla fararen hula 31 da jami'in tsaro daya sun mutu a jerin zanga-zanga da tashin hankali da aka fara tun watan Oktoba a Guinea, bisa zargin da ake wa Shugaba Alpha Conde na yunkurin yin wa’adin mulki na uku bayan kawo karshen wa'adinsa a karshen 2020. 
.